Ina tsimayen komawa kulob dina da kambun zinare -Mikel
Dan wasan tsakiyar nan na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea kuma dan asalin kasar Najeriya wanda kuma ke zaman jagoran tawagar kwallon kafar dake wakiltar kasar a gasar Olympics dake gudana yanzu haka a garin Rio na kasar Brazil ya bayyana cewar yana tsimayen komawa kungiyarsa ta Chelsea da kambun zinare.
Da yake zantawa da manema labarai, dan kwallon yace:”zan yi farin ciki sosai idan har na lashe gasar kuma na koma kungiyata da kambun.”
“Hakika zanyi iya bakin kokarina wajen ganin mun lashe gasar. Yanzu haka dai kambun zinaren shine kawai a gaban mu duka yan wasan.”
“Muna sa ran zamuyi nasara”.
Mai karatu zai iya tuna cewar mun ruwaito Mikel yana cewa mai horar da kungiyar ta sa Antonio Conte ya yi masa addu’a kafin ya taho gasar inda yace Conte din ya shawarce shi da yayi iya bakin kokarin sa wajen ganin ya taimakawa kasar sa ta lashe kambun.
Nigeria will now play Germany at the Arena Corinthians in Sao Paulo on Wednesday August 17.
The post Ina tsimayen komawa kulob dina da kambun zinare -Mikel appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.