Bala’o’i 5 dake kashe yan Najeriya
A yau a Najeriya an wayi gari da wasu bala’o’i da ka iya kuntata ma yan kasa zaman Najeriya. Yan Najeriya da dama basa jin dadin wannan yanayi.
Wani marubuci ya taba cewa komai a Najeriya na kisa. Don haka ga wasu bala’o’i guda biyar wanda ke kashe yan Najeriya
- Zazzabin Cizon Sauro
Duk da cewa an saba da jin sunan Malaria, amma fa haryau yana addabar Najeriya, alkalumma sun nuna cewa Malaria shine sanadiyyar mutuwar kasha 20 da duk mutuwar da akeyi a kasar nan.
Jama’a da dama musamman wadanda ke rayuwa a karkara suna ta fama da ciwon Malaria sakamakon kazamin yanayin dake haifar da sauro. Jama’a da dama basa iya siyan dakin sauro, saboda rashin hali, sa’annan wanda ake kaiwa asibitoci domin a raba su kyauta ga al’umma sunyi karanci.
- Ciwon shakar Iska
Ciwuka da dama da suka shafi shan iska suma suna addabar al’ummar Najeriya, kamar su ciwon sanyi, ciwon huhu da mashako. Alamun da ake gane su sun hada da karancin shakar iska, kasala, zazzabi, tari da gajiya.
Ciwon shaker iska na daukar kaso 19 na mutuwar da ake yi a kasarnan.
- Hatsarin
Abin takaici ne a ce duk da irin wayewar da aka samu a Duniya amma har yanzu daga cikin hanyar da aka fi mutuwa a Najeriya har da hatsari da ababen hawa kan yi.
Yawancin hatsarin da ake samu na da alaka da lalacewar hanyoyin mu, tayoyi marasa kyau da kuma gangancin direbobi. Rayuwar yan Najriya da dama sun salwanta sakamakon hatsari a kan manyan hanyoyin kasar nan.
- Ta’addanci da fashi
Sabon hatsaniya data taso ta tsagerun Neja Delta ya zamto abin damuwa a Najeriya, sa’annan gay an ta’adda da ake fama dasu a yankin Arewa maso Gabas wanda shima yaci rayuka da dama.
A yankin kudu maso gabas kuwa, ana fama ne da yan tada kayar baya mas bukatan a basu kasar Biafra. Anyi asarar rayuka da dama a yaki da ta’addanci dake gudana a arewa maso gabas. Sa’annan ga rikicin manoma da makiyaya da ya dabaibaye kasar nan, hadi da yan fashi da makami dake cin Karen su ba babbaki a kudu maso yammacin Najeriya.
Tsageranci a Neja Delta ya mayar da yankin wajen kashe kashen rayuka sakamakon artabu da ake samu tsakanin tsagerun da sojoji. Rudunar Sojojin Najeriya na kokarin ganin ta kawo zaman lafiya a duk fadin kasar nan, sai dai a cikin kokarin nasu rayuka da dama ke salwanta.
- Talauci
Idan da ace talauci wata cuta ce, lallai kam da a iya cewa tana tafka wa giwar Afirka Najeriya mummunar barna. Wani rahoto na shekarar 2015 da ya samo asali biyo bayan bincike da aka gudanar a shekarun 2004 da 2014 ya tabbatar da cewa akwai talakawa da dama a Najeriya.
Jerin jadawalin kasashe mafi talauci da majalisar dinkin Duniya ta fitar na da fuskoki uku da kuma ma’aunai 10 don gane matsayin talauci, a haka ne aka alkalumman da suka auna talauci ta fuskoki uku da suka hada da Ilimi, jin rayuwa, da kuma kiwon lafiya. A cewar rahoton, kasha 26 na yan Najeriya talakawa ne, amma wani rahoto na daban da bankin duniya ta fitar ta nuna cewa kashi 33 ne nay an Najeriya talakawa.
Kwanan nan ne mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osibanjo ya bayyan cewa yan Najeriya miliyan 110 na rayuka cikin talauci, duk da irin tsare tsaren gwamnatocin baya na tsamosu daga kangin talauci. Sai dai mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa ba’ayi tsare tsaren yadda ya kamata ba, sakamakon haka yasa basu amfani jama’a ba.
Talauci na daya gada cikin manyan bala’o’i dake kassara rayukan jama’a a Najeriya, sa’annan wahalhalun tattalin arzikin da ake fama dasu suna hassala matsalar. Idan aka lura, za’a gane cewa rashin aikinyi, yawan rashin biyan albashin ma’aikata, da kuma tashin farashin kayan masurufi na kai ga mutuwar mutane da dama, kai, wasu ma suke kashe kansu da kansu.
The post Bala’o’i 5 dake kashe yan Najeriya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.