Makarfi ya mayar da martani dangane da dakatar da taron jam’iyyar PDP
Sakataren watsa labarai na jam’iyyar PDP Dayo Adeyey ya fitar da wata sanarwa wadda ke bayanin matsayin da jam’iyyar PDP ta dauka danagne da dakatar da babban taron jam’iyyar da za’a gudanar nan bada dadewa ba.
Sanarwar tace “wata babbar kotu dake zaune a fatakwal, jihar Ribas ta bada umarnin ayi babban taron jam’iyyar kamar yadda ta shirya. Alkali ya baiwa yansanda, hukumar tsaro na sirri da hukumar zabe umarni da su ba jam’iyya hadin kai wajen ganin anyi taro lafiya an waste lafiya.
Bangaren Makarfi sun kara da cewa kotun dake fatakwal ya bada cikkaken umarni ne, shi kuwa kotun dake Abuja umarni na wucin gadi ya bayar, a don haka umarnin kotun fatakwal ya dara ma na kotun Abuja wadda alkali Abang ya bayar.
Da wannan, a matsayin jam’iyyar PDP na mai yin biyayya da doka, zata bi umarnin babbar kotun dake fatakwal, sai dai idan wata kotun ta kawar da umarnin.
Da wannan ne naka sanar da jama’a cewa za’a maimaita babban taron jam’iyyar PDP na 2016 kamar yadda aka shirya, kuma muna yi wa wakilai, shuwagabannin jam’iyya, hukumar zabe INEC, sauran masu ruwa da tsaki da yan’uwa da abokan arzikin jam’iyyar PDP zuwa fatakwal, kuma muna fatan gudanar da taron cikin kwanciyar hankali da nasara.
The post Makarfi ya mayar da martani dangane da dakatar da taron jam’iyyar PDP appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.