Mataimakin Mimiko, da Kwamishina sun bar PDP zuwa APC
-Yetunde Adeyanju, Kwamishinan ci gaban al’umma da hadin gwiwa na Gwamna Mimiko tayi murabus
-Ta sanar da komawar ta jam’iyyar APC a take, inda wani mataimakin Mimiko, Giwa Rasheed zai hade da ita
-Adeyanju tace akwai san zuciya a jam’iyyar PDP
Manyan mambobin biyu cikin gwamnatin Olusegun Mimiko sun shaki iskar chanji a jihar Ondo.
Yetunde Adeyanju
Bisa ga wani rahoto a jaridar The Nation, Yetunde Adeyanju, kwamishinan ci gaban al’umma da hadin gwiwa tare da Giwa Rasheed, mataimaki na mussaman ga gwamna Olusegun Mimiko, sun yi murabus zuwa jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a jiya, 15 ga watan Augusta.
Adeyanju ta bayar da takardan barin ta aiki a yammacin jiya, ta kuma bayar da wata sanarwa kafofin watsa labarai, inda ta sanar da komawan ta jam’iyyar APC.
Gwamnan jihar Ondo Olusegun Mimiko
Tace: “Bari na gwamnatin jam’iyyar Peoples Demogratic Party (PDP), sai naji wani damuwa mai nauyi ya sauka a kaina.”
KU KARANTA KUMA: Kiristoci sunfi yan ta’adda aikawata laifi – Sultan
NAIJ.com ta nuna cewa mambobin jam’iyyar PDP da dama a karamar hukumar Okitipupa na jihar Ondo sun bar jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC a kwanakin baya. Sunyi zargin cewa gwamnati mai ci a yanzu ta bari rayuwa tayi tsanani a gare su.
Wani jigon jam’iyyar Dare Agbe ne ya jagoranci basu muramus din gurin bayyana kudirinsu a wani gamuwa tare da Cif Olusola Oke, wani dan takarar gwamna a jam’iyyar APC.
A cewar masu murabu din, sun koma jam’iyyar APC ne saboda abubuwan alkhairi da Cif Oke yayi a karamar hukumar Okitipupa, a majalisar dattawa na yankin kudu.
The post Mataimakin Mimiko, da Kwamishina sun bar PDP zuwa APC appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.