Kai ba soja bane a yanzu- Sarkin Lagas ya fada ma Buhari
-Sarkin jihar Lagas, Oba Rilwan Akiolu, ya fada ma shugaban kasa Buhari da ya daina aiki a matsayin soja
-Oba Akiolu yace mstsalar tattalin arzikin Najeriya ba laifin tsohon shugabn kasa Goodluck Jonathan bane
-Yace shi da Jonathan aminai ne
sarkin Lagas, Oba Rilwan Akinolu
Rilwan Akiolu, sarkin jihar Lagas ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari kan ya daina tafiyar da gwamnati a matsayin soja. A cewar Oba Akiolu, Buhari ya gane cewa shi ba soja bane a yanzu kuma yay i aiki kamar dan farin hula, Jaridar Punch ta ruwaito.
Oba Akilu ya bayyana haka a jihar Lagas, a ranar Litinin 15 ga watan Augusta, a lokacin bude bankin Sun Trust Bank Limited, bankin kasuwanci na farko da babban bankin Najeriya ta ba Lasisi a shekaru 15. Ya nuna ra’ayinsa kamar yadda yace baza’a daura laifin halin rikicin da tattalin arzikin kasa yake a yanzu a kan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba.
KU KARANTA KUMA: Buhari na son kashe Nnamdi Kanu- IPOB sun koka
Duk da haka, Oba Akiolu, ya nemi goyon baya ga Buhari ya kuma nuna amincewa da kungiyar gwamnatin tarayya dake tafiyar da tattalin arziki karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo domin ceto tattalin arziki.
Akiolu yace: “ya zama dole dukkan mu muba shugaban kasa goyon baya kuma Ina so na shawarce shi da ya san cewa shi ba soja bane a yanzu. Bazan ji tsoron fadin haka ba. Hanyar da suke bi dan gano tushen abunda ya wuce, a zahirin gaskiya ko suna so ko basa so, ba laifin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan bane. Bazan boye gaskiyan cewa Jonathan abokina bane. Dukkan abubuwan da suka faru ba yin kanshi bane.”
The post Kai ba soja bane a yanzu- Sarkin Lagas ya fada ma Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.