Jonathan ya dawo Najeriya bayan da aka kamala zaben dayaje dubawa.
A ranar Lahadi ne 14 ga watan Agusta, Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya dawo Najeriya bayan daya kamala aikin dayajeyi, amatsayin shugaban kasashen Africa domin kula da zaben daya gunada a kasar Zambia na zaben shugaban kasa da kuma sauran zabuka nayan majalisu.
Acewar bayanin da aka sanya a yanar gizon ta kungiyar kasashen Afirica a ranar Litinin 1 gawatan Agusta ya nuna cewar Jonathan ya jagoranci sauran tawagar mambobin kasashe masu sanya ido akan ainihin sahihancin zabe a duniya domin ganin an gudanar da tsaftataccen zabe a kasar ta Zambiya.
Alokacin da zaben ke gudana a ranar Talata 9 ga watan Agusta, Jonathan din ya sanya hotunan sa a wurare daban daban domin nunama duniya.
Haka kuma ya bayyana yadda jami’an tsaron kasar ta Zambia zasuyi aiki tukuru domin ganin zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali. Idan dai za’a tuna Jonathan ya jagoranci kasashe talatin da uku masu kula da harkan zabuka dake gudana a kasashe a zaben daya gudana a kasar Tanzaniya a ranar Lahadi 25 ga watan Octoban shekaran 2015.
The post Jonathan ya dawo Najeriya bayan da aka kamala zaben dayaje dubawa. appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.