‘Yan bindiga sunyi garkuwa da mutane a Jihar Ribas
–Wasu yan bindiga sun kai farmaki jihar Ribas
–Yan bindigan sun tsare wata motan hayan sun yi garkuwa da mutane 14
–Jami’an yan sanda sunce suna gudanar da bincike
An samu wani tashin hankali a ranar juma’a 12 ga watan augusta yayinda yan bindiga suka tsare wata motan haya dauka da kimanin fasinja 14 daka birnin Fatakwal zuwa karamar hukumar Omoku in Ogba/Egbema/Ndoni.
“Hadarin ya faru ne a hanyar Elele-Ikiri-Omoku misalin karfe 4 na yamma inda yan bindigan suka fitar da fasinjojin daga cikin motan, suka bankawa motan wuta suka wuce da mutanen a motar su. Yan bindigan sun tae motan ne tamkar yan fashi yayinda motan ke kokarin shan kwana. Kakakin jami’an yan sanda, Nnamdi Omoni yace baida masaniya game da abinda ya auku . Ya fada ma manema labarai cewa : bani da masaniya a kai. Zanyi Magana akan al’amarin idan na samu cikakken bayani akai.”
A wata labara mai kama da haka, jaridar dailypost ta bada rahoton cewa babban malamin jami’ar fatakwal, farfesa John Okorie , da akayi garkuwa da shi ya samu yanci . Ofishin yan sandan jihar ribas ta tabbatar da hakan a wata hira da a hedkwatan yan sanda da ke Fatakwal.
Kakakin jami’an yan sanda, DSP Nanmdi Omoni ya bayyana hakan kuma yace babu kudin fansan da aka biya akai.
KU KARANTA : Anyi wa wata mata tsirara saboda garkuwa da mutane (Kalli hotuna)
“Omoni yace:an ceto malamin jami’ar kimanin awa 24 bayan anyi garkuwa da shi. Yayinda jami’an mu suka samu labarin,suka shiga aiki kawai. An yi jami’an kare garkuwa da mutane su bibiye yan bindigan kuma suka iya ceo shi. Ina mai fada muku cewa ba’a biya fansa ba. Kuma muna gargadi ga duk masu tayar da tarzoma a jihar ribas su bar jihar ko su daina. Saboda bazamu yarda jihar ribas ta dinga ajiye yan iska ba.”
Farfesa okori lakcara ne a bangaren injiniyanci kuma diraktan makarantan fasaha a jihar fatakwal anyi garkuwa da shine yayinda yake koma gida ranar litinin ,8 ga watan augusta.
The post ‘Yan bindiga sunyi garkuwa da mutane a Jihar Ribas appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.