Yan wasa 5 da suka samu munanan raunuka a gasar Olimfik
Yan wasa dake fafatawa a wasanni daban daban suna ta samun nasara ta hanyar cinye kyaututtuka iri iri a gasar Olimfik dake gudana a Rio ta kasar Brazil.
Sai dai akwai wasu yan wasan da suka samu munanan raunuka iri iri, kamar su karayan kafa, karayan gadon baya, da kuma kujewa a wuya da kirji. Ga biyar daga cikin wadanda suka fi samun raunuka munana.
1. Samir Ait Said: Samir mai shekaru 26 dan kasar Faransa ya samu karayar kafa a yayin wasan tsalle da yake yi, karayar ta afku bayan ya diro a kasa, sai kashin kafarsa ta karkace daga mazauninta.
2. Andranik Karapetyan: Andranik na daya daga cikin shahararrun masu daga karfe a duniya, sai dai dan kasar kasar Armenia mai shekaru 20 ya fice daga gasar bayan ya samu mummunar targade a gwiwar hannunsa a yayin da yake kokarin daukan karfe.
3. Ellie Downie: Ellie sabuwar yar wasa ce dake wakiltar kasar Birtaniya a wasannin tsalle tsalle, ta shad a kyar bayan fa fado a wuya.
4. Annemiek van Vleuten: an garzaya da Vleuten dan wasan tseren keke ne dan kasar Netherlands asibiti don samun kulawar gaggawa biyo bayan hadarin da ya rutsa da ita a yayin da take tuki wanda yayi sanadiyyar karaya uku a kashin bayan ta.
5. Joost van der Burg: Jurg na wakiltar kasar Netherland a gasar tukin keke na cikin rumfa, sai dai ya samu hatsarin da yayi sanadiyyyar kujewarsa, wanda har fatar jikinsa ta makale a kasa. Amma shima an ruga da shi asibiti don samun kulawa.
The post Yan wasa 5 da suka samu munanan raunuka a gasar Olimfik appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.