Barista Umsan yayi murabus don yin takara a PDP
Daya daga cikin yan kwamitin riko na jam’iyar PDP yayi murabus daga kasancewa memban kwamitin don yin takarar kujerar sakataren watsa labarai ta Jam’iyar. Dan takarar ya samu goyon bayan wasu kungiyoyi.
A wata sanarwa da Pa Ibrahim Adama ya sanya ma hannu, kungiyar tasu tace kujerar da Usman ke nema nada matukar muhimmanci don haka ake bukatar jajirtaccen mutum ya rike ta. Barista Kabir tsohon mai baiwa jam’iyar PDP shawara a kan harkan shari’a na yankin Arewa ta tsakiya ya yi amfani da matsayinsa na memba a kwamitin riko ta jam’iyar inda yayi tafiya da al’umma talakawa, kuma yana girmama dattijan jam’iya.
“a wannan lokacin, irin nasarorin da ya samu yasa ya zamto mafi ingantaccen dan takarar wannan kujerar, sa’annan irin rawar da ya taka a kwamitin riko na kasa ya wuce misali.
“a cewar Pa Ibrahim Adama, Barista Kabir ya taka rawa sosai a wajen dawo ma da PDP kujerunta a majalisar dattijai na mazabun kogi ta gabas da ta tsakiya, sa’annan yana tare da jam’an sa duk da irin ayyukan da yake gudanarwa a matakin kasa. “Barista Kabir zai zamto sabon muryar PDP, sa’annan ba shi da wani guntun kasha a gindinsa.”
The post Barista Umsan yayi murabus don yin takara a PDP appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.